Gwamnatin jihar Bauchi ta rabawa membibin kungiyar ‘M.A Social Media Support Group’ kayan aiki a yayin wani taron bita da gwamnatin ta shirya a jiya Lahadi bayan kammala gangamin tarbar Gwamna a hutun da ya je na makwanni uku.
Taron bitar wanda ya sami halartar membobin kungiyar sama da 150 daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar, babban mai tallafawa gwamnan kan harkar yada labarai da sadarwa Kwamred Sabo Muhammad ne ya jagoranci wannan bita tare da abokan aikin sa da suka hada da Kakakin Gwaman Abubakar Al-Sidique. Sai mai tallafawa Gwamna kan harkar sadarwa Alhaji Shamsuddeen Lukman Abubakar da takwaran sa Honarabul Muhammad Nuraddeen, sai mai tallafawa Gwamna kan yada labarai Alhaji Kabir Nuru Lemi.
Babban bako a wajen bikin shine mai tallafawa Shugaban Kasa kan harkar sabbin kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, wanda Bashir Abdullahi El-bash ya wakilce shi.
Bayan kammala jawabai ne a ka shiga rabawa Membobin kungiyar wayoyin hanu da kudaden Data.
Ita dai wannan Kungiya tana da Iyaye daga ko ina a sassan jihar Babban Uban ta shine Engr. Alh Ali Kumo (Sardaunan Doma, Bunun Akko) sai Uban Kungiyar daga Bauchi ta Arewa Hon. Tijjani Muhammad Aliyu Shugaban masu rinjaye a majalisar jihar Bauchi sai Uban Kungiyar daga Bauchi ta tsakiya Hon. Bappa Aliyu Misau (Sarkin Yamman Misau) sai kuma Uba daga Bauchi ta Kudu Hon. Ibrahim Bala Hassan Dan Majalisar jiha mai wakiltar Duguri da Gwana.
An kammala taron cikin nasara daga bisani a ka rufe taron da addu’a.