Gwamnatin Jihar Edo Ta Haramta Kiwo Ma Tsawon Wata Uku


Gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki ya haramta yin kiwo a wasu yankunan jihar har na tsawon kwanaki 90 a wani mataki na shawo kan zubar da jinin da ake yi sakamakon rikicin makiyaya da manoma.

Gwamnan ya ce, an kafa wani kwamitin tsawatarwa wanda ya kunshi sojoji, ‘yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya, ‘yan Banga da Mafarauta wadanda za su farauto miyagun makiyaya da suka addabi wadannan yankunan.

You may also like