
Gwamnatin jihar Enugu ta bada umarnin daukar malaman makaranta 700 karkashin hukumar kula da ilimi tun daga tushe ta jihar wato ENSUBEB.
Kwamishinan Ilimi, Farfesa Uche Eze shine ya bayyana haka ranar Laraba a Enugu lokacin da yakewa manema labarai jawabi bayan taron majalisar zartarwa ta jihar.
Eze ya ce malam makarantun firamare 42 ne suka rasa rayukansu lokacin da suke bakin aiki a shekarar da ta gabata.
Kwamishinan wanda bai bayyana dalilin mutuwar malaman ba ya kuma bayyana cewa wasu 797 ne za su yi ritaya a ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.
Ya ce hakan ya haifar da wani gibi dake buƙatar cike wa.
Eze ya ce malamai 1320 aka dauka aiki a shekarar 2016, bayan kammala ɗaukar malaman da za a yi anan gaba za a sake rarraba malaman zuwa kowanne sassa na jihar domin samun daidaito.