Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Raba Motoci Domin Kai Mata Masu Juna Biyu Asibiti KyautaGwamnatin jihar Jigawa, jarkashin jagorancin Badaru Abubakar, ta raba motoci ashirin a fadin jihar domin yin amfani da su wajen kai mata masu juna biyu zuwa asibici. 
Mataimakin Gwamnan jihar, Barista Ibrahim Hassan Hadejia, wanda shine ya wakilci Gwamnan, ya ce an raba motocin ne domin daukar mata masu juna biyu zuwa asibici kyauta, domin magance yawan mace-macen mata a yayin haihuwa. 
Barista Ibrahim Hassan Hadejia ya kuma gargadi direbobin da su yi aiki da motocin kamar yadda gwamnati ta tsara, domin a cewar sa duk direban da aka samu da amfani da motar ba ta hanyar da ta dace ba, to doka za tayi aiki a kansa. 
Daga karshe kwamishiniyar mata, Hajiya Ladi Dan Sure, ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa dangane da irin kulawar da take baiwa matan jihar.

You may also like