A karshe gwamnatin jihar kaduna ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin da takafa domin sake duba yawan yawan hakimai da dagatan dake jihar.
Bayan amimcewa da rahoton, wanda ya bada shawarar rage hakimai da dagatai 4766 yanzu dai gwamnatin jihar ta amince da hakimai 77 da kuma dagatai 1,429 kamar yadda suke kafin shekarar 2001.
Yawan hakiman yadadu da 390 bayan da aka kirkiri 313,yayin da yawan dagatai yadadu da 5,882.
Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji ja’afaru Sani, ya bayyana haka a wani taron manema labarai inda yace anyi haka ne domin ragewa kananan hukumomi nauyi.
Gwamnati tace ta tattauna da majalisar sarakunan jihar kafin ta zartar da shawarar da kwamitin ya bayar.
Kwamishinan yace kirkirar wasu masarautun da akayi a shekarar 2001 ya kara yawan hakiman da ake dasu tare da ma’aikatan da suke aiki a ofisoshinsu mutum 2700 wanda duka kananan hukumomi ne suke biyansu.
Sai dai kwamishinan yace wannan sauyin bazai shafi sarakuna 32 da jihar take dasu.