Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Umarci Jami’an Tsaro Su Binciko Wadanda Suka Kashe Wasu Fulani Biyu
KADUNA, NIGERIA – Rahotanni dai sun ce wasu Fulani biyu ne su ka shiga Birnin Gwari sayayya sai wasu suka fara zarginsu, wanda hakan ya sa aka kira jami’an tsaro, amma sai mutane su ka afka wa jami’an tsaron, inda suka kwace mutane biyun da ake zargi, sannan su ka kashe su kuma su ka kona su.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya ce gwamnan Jihar Kaduna ya yi Allah wadai da wannan daukar doka a hannu.

Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya sun ce irin wannan daukar doka a hannu na da hadari ga al’umma baki daya.

Saurari cikakken rahoton daga Isah Lawal Ikara:

You may also like