Gwamnatin Jihar Kano Da Kamfanin RUYI Na Kasar China Za Su Gina Kamfanin Samar Da Tufafi Na Dala Miliyan 600 A KanoA cikin ziyarar aiki da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya je yi a kasar China da ‘yan tawagarsa a  jiya ya jagoranci sanya hannu akan yarjejeniyar gina wannan Masanaanta ta Sarrafa Tufafi akan jimlar kudi Dala Miliyan 600 ne da kamfanin RUYI Na Kasar China wanda ya kware akan harkar Tufafi.

Kamfanin RUYI sun yi Alkawarin fara wannan aikin acikin wannan Shekara wanda idan ba’a manta ba watanni uku baya sukazo Jihar Kano kuma tuni Gwamnatin Jihar Kano tabasu waje dazasu gina wannan Masana’anta wanda idan suka Kammala babu irinta duk Afrika.

Kamfanin sun bayyana  samar da Wuta me aiki da hasken rana don gudanar da wannan Kamfani a Jihar Kano inda kuma suka yi alkawarin.

You may also like