Gwamnatin Jihar Kogi Ta Sanar Da Gobe Litinin A Matsayin Hutun Murnar Dawowar Shugaba Buhari


yahaya-bello-750x430
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ware gobe Litinin, 21 ga watan Agusta a matsayin hutu da kuma godiya ga Allah bisa dawo da shugaba Muhammadu Buhari da Allah ya yi gida Nijeriya daga London cikin koshin lafiya
Daraktan yada labaran gwamnan, Kingsley Fanwo ne ya fitar da sanarwar a yau Lahadi a garin Lokoja, babban birnin jihar
Sanarwar ta ce hutun wani yunkuri ne da jihar ta yi na dada tabbatar da goyon bayanta ga shugaba Muhammadu Buhari
“Muna fata ‘yan jihar Kogi za su yi amfani da wannan hutu na gobe Litinin wajen yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu’o’in nasara da koshin lafiya yayin da ya karbi aikin gyatta kasarmu,” sanarwar ta ce
Gwamna Yahaya Bello ya godewa ‘yan jihar bisa ci gaba da goyon baya da suke nunawa gwamnatin Baba Buhari da kuma fita da suka yi tsaki da kwarkwata wajen yi wa shugaba Mhammadu Buhari barka da zuwa a can Abuja jiya

You may also like