Abdullahi Sani-Oseze, shugaban hukumar fansho ta jihar Nassarawa ya ce gwamnatin jihar ta kara mafi ƙarancin kuɗin fansho zuwa naira ₦5000.
Sani Oseze ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ranar Asabar a lafiya babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta yi haka ne domin kyautata rayuwar yan fansho duba da halin yanayin tattalin arziki da muke ciki.
Shugaban yace wasu ma’aikatan da suka yi ritaya kafin a aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi a jihar suna karɓar karancin kudin fansho da ya kama daga kan ₦1000.
“Saboda haka mun duba halin da irin wadannan yan fansho ke ciki muka kuma mikawa gwamna Umar Tanko Almakura rahoton haka ya kuma bada umarnin da a sake daga mafi ƙarancin fansho da ake biya a jihar.” Ya ce.
Sani Oseze ya ce hukumar na daukar mataki domin magani wasu matsaloli na wasu yan fansho wadanda basu taba amfana da biyan kudin da ake ba tun farko fara gwamnatin Al-Makura a shekarar 2011.