Gwamnatin Jihar Nejar Najeriya Ta Kori Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazan Jihar
NIGER, NIGERIA – Gwamantin jihar Nejar dai ta dauki wannan mataki ne na korar sakataren hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Alhaji Umar Makun Lapai daga kan mukaminsa, a dai-dai lokacin da tsohon sakataren ke kasa mai tsarki domin ci gaba da shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Koda yake dai babu cikakken bayani da gwamnatin jihar Nejar ta yi game da dalilin korar wannan sakatare, amma a wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamanatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ta nuna maye gurbinsa da wani sabon mai duba harkokin Alhazai.

Tuni dai al’ummar jihar Nejan suka fara bayyana ra’ayinsu akan sabon sakataren.

Sabon sakataren hukumar Alhazan jihar Nejan Muhammad Awwal Aliyu ya kuma bada tabbacin yin aiki tukuru domin kula da jin dadin maniyyatan jihar da ake sa ran yawansu ya haura 4000.

A yanzu dai maniyyata daga jihar Nejan na cike da fatan ganin an yi jigilarsu daga filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Minna, a maimakon jigilarsu ta Abuja kamar yadda ya faru a lokacin aikin Hajjin bara.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like