Gwamnatin Jihar Sokoto Tayi Belim Wasu Fursunoni Guda 20 Kan Naira Milyan 2.Gwamnatin jihar ta biya musu tarar ne ta hannun ma’aikatar lamurran addini ta jihar, domin a sake su su koma cikin iyalansu kasancewa ba su da kudin da za su biya wa kansu tarar. 
Gwamnan jahar Aminu Waziri Tambuwal  wanda kwamishinan ma’aikatar raya karkara Abdullahi Mai Gwandu ya wakilta a wurin taron, ya ce wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin sa ke yi na rage wa al’umma damuwar matsalolin yau da kullun da kan taso. 
Ya yi kira gare su da su guji saka  kansu cikin duk wani abu da zai sa a sake mai da su gidan Yari, maimakon hakan yace su koma makaranta ko su samu sana’ar yi kasancewar su matasa, domin su zamo masu amfani ga kansu da al’umma.
Wadanda aka saka din sun yi godiya da alkawarin zama ‘yan kasa nagari. Kowannen su an ba shi kudin mota don komawa garinsu. 
Wannan taron an yi shine a mazaunin kwamitin Zakka da wakafi na jihar Sokoto wanda Malam Mawal Maidoki ke jagoranta.
A lokacin taron an raba kayan wa’azi, rabarmi ga kungiyoyin Addinin musulunchi, Limamai, malammai, makarantun islamiyya, na Allo, mudun awo ga kungiyoyin masu sayarda abinci, na gundumomi  da sauransu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like