Gwamnatin Jihar Sokoto Zata Kashe Miliyan 88 Wajen Ciyarwar Azumi Gwamnatin jihar Sokoto ta ware naira miliyan 88, domin ciyarwar azumi da kuma tallafawa  masu karamin karfi.

Kwamishinan al’adu da walwalar Jama’a, Surajo Gatawa, ya bayyana haka a wurin taron da ma’aikatu  suke bayyana nasarorin da suka samu,domin bikin cikar gwamnan jihar Shekaru biyu da kama aiki.  

A cewar Gatawa tallafawar zata sa suma masu karamin karfi suyi azumi cikin walwala.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta samu nasarar yiwa masu tabin hankali su 20 magani akan kudi naira miliyan 3.

Kwamishinan yace miliyan  daya da dubu dari bakwai aka kashe wajen yiwa wasu marayu aure. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like