Gwamnatin Jihar Zanfara Ta Sassauta Dokar Hana Fita Albarkacin Ramadan
Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a daukacin jihar ne sakamakon barnata dukiya da sunan murna da wakilai da ‘yan jam’iyyar PDP mai adawa suka yi.

Sai dai a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Magaji Dosar ya fitar a ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar ta ga ya dace ta daidaita lokacin dokar hana fita a fadin jihar da gwamnati ta sanya domin dakile yawaitar hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da satar kayan jama’a da barnata dukiyar gwamnati da na jama’a da sunan murnar samun nasarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna da aka kammala a jihar.

Sanarwar ta ce, “A yanzu dokar hana fitar ta koma daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safe, ta fara aiki daga ranar Alhamis, 23 ga Maris, 2023. Hakan na nufin baiwa mutane damar halartar ibada da gudanar da ayyukan da ake bukata a cikin watan Ramadan.”

Sanarwar ta yi gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani hali na rashin da’a ba, kuma za ta dau mataki mai tsauri a kan duk wanda aka kama yana kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar.

Sanawar ta shawarci ’yan siyasa da su ja kunnen magoya bayansu don guje wa tashin hankali, su kuma kasance masu zaman lafiya domin samun hadin kai, ci gaba da ci gaban wannan jiha tamu.

-Daily PostSource link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like