Gwamnatin Kaduna Ta Bada Umarnin Cafke Wani Fulani


Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya bayar da umarni ga jami’an tsaro da su kama wani bafulatani mai suna Haruna, wanda ake zargi da harin da aka kai kan al’ummar masarautar Chawai da ke karamar hukumar Kauru a kudancin Kaduna

El Rufa’i ya bukaci Haruna da ya mika kansa ga shugaban fulanin sashensa (Ardo) ko kuma ya fuskanci cukwuikuya daga jami’an tsaron jihar ta Kaduna

El Rufa’i ya ci gaba da cewa, za mu kama Haruna don ya bayyana mana dalilinsa na haddasa wannan ta’asa da ta yi sanadiyar rayuka da dukiyoyin al’umma

Fulani dai sun kai hari ne akan al’ummatan garuruwan-Kigam da Unguwar Rimi da Unguwar Magaji wanda harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 38 tare da jikkata wasu da dama

You may also like