Gwamnatin Kaduna Ta Haramta Ayyukan ‘Yan Shi’a a Jihar


 

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta haramta ayyukan kungiyar Shi’a a fadin jihar, inda take cewa an dauki matakin ne domin ganin zaman lafiya da tsaro sun kankama a fadin jihar.

Wata sanarwa da Kakakin Gwamna Nasir Rufai ya bayar a kaduna bayan taron majalisar zartaswan jihar na cewa Majalisar ta tattauna sosai kafin ta dauki wannan mataki.

 

Matakin na zuwa ne bayan an kwashe watanni da kisan ‘yan Sh’ia sama da 300 a garin Zaria yayin wata aragama da sojan kasar.

Kungiyar ta Shi’a dai ta ki bayyana gaban komitin da Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin bin diddigin abinda ya faru.

‘Yan kungiyar na bukatar dole a saki jagoran su Ibrahim El-Zakzaky da ake tsare dashin watanni da yawa hannun jami’an tsaro.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like