Gwamnatin Kaduna Ta Ja Kunnen Masu Tayar Da Fitina


 

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa daukar doka a hannu da wadansu matasan jihar Suka yi akan mabiya akidar Shi’a a ranar Laraba da ta gabata bai dace ba, kuma ba za ta zura ido tana kallon wasu na neman yi wa zaman lafiya karan-tsaye ba.
Gwamnatin ta yi wannan gargadi ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Gwamnan jihar na musamman kan harkar yada labarai, Samuel Aruwan ya sanya wa hannu. Inda ya ce, Gwamna El-Rufai ya umurci jami’an tsaro su kama duk wani wanda ke kokarin ta da zaune tsaye a jihar.
Aruwan ya ci gaba da cewa, gwamnatin za ta binciki abin da ya faru, kuma ta hukunta duk wadanda aka samu suna da hannu a wannan mummunan abu.
Aruwan ya ce, “gwamnati ta la’anci wannan abin takaici da ya faru, sannan tana jajanta wa wadanda abin ya shafa. Don haka gwamnati na yin gargadi da kakkausar murya ga duk masu wannan dabi’a, tare da bayyana cewa ba za ta zura ido ana wadannan abubuwa ba.”

You may also like