Gwamnatin Kaduna Ta Musanta Batun Cewar Ta Biya Fulani Makiyaya Kudi Domin Daina Kai Hare-Hare A Kudancin Jihar



Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata labarin da ake yadawa na cewar wai ta biya kudi ga wasu gungun Fulani Makiyaya dake yankin Kudancin jihar domin su daina kai hare-hare a yankin.
Da yake jawabi gaban manema labarai mai magana da yawun gwamnatin jihar Mista Samuel Aruwan, ya bayyana wannan labari a matsayin kanzon kurege da wasu suka kirkira domin neman shafawa gwamnatin Malam Nasiru El Rufa’i bakin fenti.
Samuel Aruwan ya bayyana cewar gwamnatin Jihar karkashin Nasiru El Rufa’i, tana iya bakin kokarinta na ganin zaman lafiya ya samu a yankin kudancin Kaduna dama jihar gaba daya, ta hanyar tattaunawa da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, sabanin bayanan da ake yadawa na cewar tana biyan kudi ga wasu.
Mai baiwa gwamnan shawara ta fuskar yada labarai ya cigaba da cewar, ko alama gwamnatin jihar bataji dadin kalaman da suka fito daga bakin Sanata mai wakiltar kudancin Kaduna a majalisar Dattawa Mista Danjuma Lar, na zargin gwamnatin El Rufa’i da marawa ayyukan ta’addanci baya ba, inda ya bayyana kalaman sanatan a matsayin zargi maras tushe wanda kuma zai iya zama barazana ga zaman lafiyar jihar ta Kaduna.
Samuel Aruwan ya kuma bukaci ‘yan jaridu a fadin jihar dasu taimaka wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a fadin jihar, su guji yada labarai wadanda basuda tushe ballantana makama, domin wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar gaba daya.

You may also like