Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’I ta bayyana cewar zata kashe kudi har Naira Biliyan 33 domin gudanar da manyan ayyuka a bangaren harkar ilimi a shekarar 2018.
Kamfanin Dillacin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa batun hakan na kunshe ne a ciki kasafin kudin shekarar 2018 na Gwamnatin jihar.
Bayanin kasafin kudin ya nuna cewar adadin kudin da za’a kashe yana kasa da wanda akayi kasafi na shekarar 2017 inda aka kiyasta kashe Naira Biliyan 44.8.
Kasafin kudin ya nuna cewar Naira Biliyan 20 zasu tafi kai tsaye ga Ma’aikatar ilimi Kimiyya da Fasaha, sannan Naira Biliyan 13 za’a kaisu ga hukumar bayar da ilimin Firamare ta Jihar Kaduna, da manyan Makarantu na jihar.
Ana sa ran Ma’aikatar ilimi za ta kashe Naira Biliyan 6.3 wajen ciyar da yaran makarantu na jihar, Makaratun Islamiyya dana karatun Al Kur’ani, sannan da karin wasu Makarantun Kwana 31 dake jihar. Kamfanin Dillacin labaran Nijeriya ya bayyana cewar Naira Biliyan 6.3 da za’a kashe suna kasa da Naira Biliyan 14.7 wanda aka shiryawa shirin a shekarar 2017.
Kamar yadda aka tsara Makarantun Firamare dana Sakandire dake fadin Jihar ,ayyukan sabunta gine ginen su da kayyakin ayyuka da za’a samar musu za’a kashe Naira Biliyan Biyar, sannan shirin hadin gwiwa na bunkasa ilimi na kasa da kasa zai ci Naira Biliyan 1.9 sabanin Naira Biliyan Biyu da aka tsara a shekarar 2017.
Hakanan takardar kasafin kudin ta bayyana cewar Ma’aikatar ilimi da hadin gwiwa Bankin Musulunci (IDB) za su kashe Naira Miliyan 761.7 domin gyaran Makarantun Sakandare na Kimiyya da Fasaha guda Shidda dake fadin Jihar.
Hakanan an ware Naira Biliyan Daya domin sayo kujeru da Tebura a makarantun Sakandare dake jihar, da kuma Naira Miliyan 511 domin samar da kayan sawa na Makarantun.
Sannan an ware Naira Miliyan 377 domin gudanar da shirin ilimantar da malaman Makarantun Gwamnatin Jihar, a Karkashin shirin hadin gwiwa na Gwamnatin kasar Birtaniya na habaka cigaban ilimi (DFID).
Hakazalika kayayyakin da za’a samar na bangaren ilimin Kimiyya da fasaha zai lashe Naira Milyan 177.8, sannan Naira Miliyan 400 za’a kashe su wajen samar da Littatafai, sannan aka kashe Naira Biliyan 2.3 wajen aikin katange dukkanin Makarantun.
Za kuma a kashe Naira Miliyan 138 domin gyaran Na’urorin Kwamfuta da dakunan gudanar da bincike, sannan za’a samar da Karin wasu manyan Na’urorin Kwamfuta har guda 20 ga Makarantun Sakandare 50 dake jihar.
Sannan an ware Naira Miliyan 50.2 domin cigaban manyan cibiyoyin koyon ilimin Kwamfuta uku dake mazabar ‘Yan Majalisar Dattawa uku dake fadin jihar, sannan bayanin kasafin kudin, ya bayyana cewar za’a kashe Naira Biliyan 50 wajen sayen Tankokin ruwa dana dahuwa, sannan da samar da na’urorin dumama wuri a makarantun kwana 29 dake fadin jihar ta Kaduna.
Sannan da akwai karin Naira Miliyan 14 wadanda aka ware domin da tsare tsare da samar da kayayyakin da ake bukata na aikin taron karawa juna a Hedikwatar Ma’aikatar ilimi.
Kasafin kudin ya ware Naira Miliyan 65.5 domin gudanar da ayyukan zamani na yada labarai da ilimin Kimiyya ta sadarwa (ICT) da Cibiyoyin yada bayanai na saurare da na kallo.
Hakanan ilimin kere kere da fasahar zamani an ware mishi Naira Miliyan 2.5, sannan Makarantun fasaha da koyar da dabarun zamani an ware Naira Miliyan 120.
Sannan ga manyan cibiyoyin ilimi dake jihar kasafin kudin ya ware Naira Biliyan 2.1 ga Jami’ar Jihar, Naira Biliyan 1.5 ga Kwalejin Ilimi dake gidan Waya, sannan Naira 670 ga Makarantar Kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli Zariya, sannan an ware Naira Miliyan 110 ga Kwalejin koyon aikin unguwar zoma dake Kaduna.
Sannan sauran manyan ayyuka da aka sanya gaba, an ware Naira Miliyan 113 ga Kwalejin koyon aikin kiwon lafiya ta Shehu Idris da Kimiyya da fasaha, sannan za’a baiwa Kwalejin koyon aikin jinya da unguwar zoma dake jihar Naira Miliyan 182.