Gwamnatin Kano bata da niyyar korar malaman makarantu


Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya ce gwamnatin jihar bata yin wani shiri na korar malaman makaranta dake jihar.
Da yake mai da martani kan wata jita-jita da ake yadawa cewa gwamnatin jihar na shirin korar malaman makarantu, kwamishinan yace jita-jitar ba gaskiya  ba ce, neman fitina ne, ba ta ma dace ba.

Garba yace,kwamishinan Ilimi na jihar kuma mataimakin gwamna, Hafiz Abubakar bai taba rubuta takarda ba akan haka ballantana ya gabatar da batun a gaban majalisar zartarwa.

” A iya sanina babu wani lokaci da aka taba tattauna wannan batun a matakin gwamnati. Saboda haka gwamnatin Kano mai ci yanzu bata da wani shiri ko wane iri na korar malamai ko kuma kowane irin ma’aikaci a jihar.” Ya ce.

Kwamishinan yayi ƙarin haske kan  cewa a maimakon haka gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin malaman firamare su 25000 domin samun takardar shedar aikin malunta ta NCE da kuma karatun digiri.

You may also like