Gwamnatin Kano Na Yunkurin Yi Wa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Kafar UnguluSakataren gwamnatin jihar Kano Usman Alhaji da kuma kwamishinan Shari’a Haruna Falali, na yunkurin yi wa Hukumar yaki da cin hanci da sauraron koke-koke kafar Ungulu sakamakon tona asirin wasu Manyan jihar da shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya yi a kwanakin baya.

 Bankado badakalar filaye da Kwamishinan muhalli, Bibi Farouk da dan marigayi Sarkin Kano, Ahmed Bayero suka yi na daga cikin abinda ya kada hantar manyan jihar suka fara tunanin gara su yi wa tufkar hanci kada asirin su ya tonu.

 Wannan ya sa sakataren gwamnatin jihar ya rubutawa Gwamna Ganduje takarda yana neman ya sa kakakin Majalisar dokokin jihar Alhassan Rurum, su yi doka a mayar da ikon hukumar karkashin ofishin sa.

 Bayan a sashe na 8 na dokokin hukumar za ta ci gashin kanta ne ba wai ta zama ‘yar amshin shata ba.

You may also like