A zamanta na ranar Laraban da ya gabata, majalisar zartarwar jihar Kano bisa jagoranci gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da kashe wuri na gugan wuri har naira biliyan 3.8 don samar da ababen more rayuwa a fadin jihar da kewaye.
A cewar kwamishinan al’adu, matasa da yada labarai ta jihar, Malam Muhammad Garba, kaso 45 cikin 100 na adadin kudin da majalisar ta amince za ta kashe ya zo ne daga kudaden da jihar ta samar wa kanta ta hanyar haraji da sauran hanyoyin samun kudin shiga na jihar.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, naira miliyan 870 cikin kudaden, za a kashe su wajen samar da tituna 6 a karkara daban-daban a kokarin gwamnatin Kano a karkashin gwamna AbdullahiUmar Ganduje na raya karkara.
Titunan da za a yi aiki a kai sun hada da: Titin Takai zuwa Albasu mai tsawo kilomita 12.5, Titin Dawakin Tofa zuwa Bichi mai tsawon kilomita 8.5, sai Titin Garun Malam zuwa Agalawa mai tsawon kilomita 11.2. Sauran titunan sune titin Bebeji zuwa Zarewa mai tsawon kilomita 7.8, sai Makoda zuwa Maitsidau-Tsangaya mai tsawon kilomita 8.9, sai kuma titin Jogana zuwa Nahuce mai tsawon kilomita 7.5
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta amince bayar da aikin titin Kofar Dan Agundi zuwa Fadar Mai Marataba Sarkin Kano akan kudi Naira miliyan 239.
Haka kuma, majalisar ta sanya hannu akan aikin titin Dungurawa zuwa Dawakin Tofa akan naira miliyan 615, sannan titin Ungogo zuwa Minjibir akan naira miliyan 350
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, an ware miliyan 280 don baiwa matasa 100 maza da 50 mata horo na musamman kan zama injiniyan motoci a kamfanin Fijo (Peugeot Automobile Nigeria) Kaduna. Kuma da zarar sun kammala samun horon, gwamnati ta ware naira miliyan 16 don basu jari
Haka kuma gwamnati ta ware naira miliyan 183 don gyara dakunan karatu mallakar gwamnati har 18 tare da gina wasu, sannan kuma za a kashe naira miliyan 21 don samar da kaladar musulunci kwafe dubu 30 ta shekarar 1438
Kwaminan ya kuma bayyana wa manema labarai cewa, gwamnatin ta amince da daukar kwararu don bada shawara kan yadda za a fidda taswirar digar jirgin kasa mallakar gwamnatin Kano mai inganci