Gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje a yau Lahadi take shirin bikin aurar da zawarawa 1,520 a kananan hukumomi 44 na jihar karkashin kwamishinan Ma’aikatar kananan hukumomi, Honarabul Murtala Sule Garo,
Wanan Daurin Aure ana gudanaar dashii adukkannin masalatan Juma’a dake kananan hukumomi 44.
Wakilinmu ya halarci daya daga cikin masallatan da aka daura auran wato masallacin Isiyaka Rabi’u dake Goran Dutse, inda aka daura auran mata 38.
Limamin masallacin Kofar Mata, Malam Nasir Adam shine ya fara jagorantar auran, daga bisani malamai suka ci gaba. Mataimakin gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar shine ya jagoranci taron.
An biya sadakin dubu ashirin ga kowacce amarya.