Gwamnatin Kano Ta Kammala Horar Da ‘Yan Fim Din Hausa Na Tsawon Makonni UkuA yau Juma’a ne aka kammala horar da masu harkar shirya finafinan Hausa na tsawon makonni uku wanda ya gudana  karkashin shugaban hukumar tace Finafinai Malam Ismaila Na’Abba Afakallah Bisa sahalewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Mutane 450 ne suka amfana da shirin a bangarori kamar haka.

1.Masu Bada Umarni (Directors)
2. Jarumai (Actors & Actress)
3. Masu Tacewa (Editors)
4. Masu Daukar Hoto (photographrs)
5. Masu Shiryawa (Producers)
6. Masu rubuta fim (scripting)

Jarumi Ali Nuhu shine babban bako da ya hallaci ranar karshe domin yi musu fatan alheri da kuma fatan nasara.

You may also like