Gwamnati Kano ta musanta jita-jitar da ake yayatawa a kafofin Sadarwar Zumunta cewa mayakan Boko Haram sun kai hari wani Makaranta kwana tare da arcewa da wasu dalibai.
Kwamishinan Yada Labarai Matasa da Al’adu, Muhammad Garba ya ce wasu marasa kishin kasa ne ke yayata wannan jitar inda ya nemi al’ummar kan su yi watsi da wannan jita-jitar.