Dr. Yunusa Adamu Dangwani kwararren likita ne wanda yakai kololuwa a harkar likitanci, shine ya rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano kafin daga baya a nadashi Kwamishinan ruwa na jihar Kano daga shekarar 2011-2015 lokacin mulkin Kwankwaso.
Dr. Dangwani yana daya daga cikin yan sahun gaba a cikin manyan mutane na jihar Kano da suka yarda da tafiyar Kwankwasiyya kuma suka yarda su kasance da Sanata Kwankwaso a duk wani runtsi na siyasa.
Biyayya, goyon baya da gudunmawa da yake bawa tsarin tafiyar Kwankwasiyya a kasa ya janyo masa bakin Jini matuka daga wajen gwamnatin jihar Kano da kuma Gwamna Ganduje shi kansa.
Gwamnatin Kano tayi iya kokarinta domin taga ta sameshi da wani laifi wanda ya shafi aikin da yayiwa gwamnati a baya amma hakanta yaki ya cimma ruwa, ansha kafa kwamitocin bincike domin kawai a sameshi da laifi komai kankantarsa ayi amfani dashi a tozartashi amma tarkonsu ya gaza kamashi.
Rashin samun kwakkwarar hujja da dalilai da gwamnati zatayi amfani dasu wajen cin zarafinsa yasa suka canja tunaninsu daga neman hujja zuwa yin kazafi a gareshi.
A Wannan gabar nake Kara shawartar hukumar tsaro ta DSS da Lallai su Lura sosai suyi takatsantsan kada su yarda wani mutum yayi amfani dasu ya batawa wani suna kokuma ya bata musu tsarin aiki domin biyan bukatar siyasa.
Ayi binciken kwakwaf a gano Mai laifi a hukuntashi ko wanene shi sannan duk wanda ba’a sameshi da laifi ba ayi kokarin yimasa adalci tare da neman afuwarsa.
Ita kuma gwamnatin Kano ya kamata ta sani, takurawa, cusgunawa tare da matsawa abokan adawa ba shine mafita a gareta ba, abu guda daya dazai zamo mafita a gareta shine azo a cikawa talakawan Kano alkawuran da akayi musu lokacin Yakin neman Zabe.
Daga karshe Munaso al’umma ta sani duk wani yanayi da Dan uwanmu ya shiga muna tare dashi, Don haka a Yanzu ma muna tare Dr. Dangwani muna masa addu’a ta Fatan alkairi da addu’ar Allah ya watsa aniyar makiyansa.