‘Yan kasuwar Sabon Gari dake Kano sun samu gudunmawar Naira Milyan N500 daga Gwamnatin jihar domin rage radadin asarar da suka tafka a gobarar da taci kasuwar a farkon sheakarar nan.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a wajen bikin sanya hannu kan wata yarjejeniyar gina katafariyar alkaryar Kasuwanci a jihar Kano da wani kamfanin jihar mai suna, Brian and Hammers Ltd.
Gwamnan ya ce an samo kudaden ne daga cikin asusun kudaden shigar da jihar ke samu.
Ya ce tuni sun kafa wani kwamiti a karkashin hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, da zai nemi gudunmawa da za’a taimaki ‘yan kasuwar.
Haka Kazalika ya ce sun karbi rahoton kwamitin Shara’a da Gwamnatin jihar ta kafa domin binciken musababbin tashin wutar. Yana mai bada tabbacin zasu yi amfani da shawarwarin da kwamitin ya bayar.
Gwamna Ganduje ya cigaba da bayyana cewa Gwamnatinsa zata cigaba da aiwatar da manyan ayyuka domin bunkasa jihar a fannin kasuwanci. Sannan ana gina hanyoyi a kasuwar Kantin Kwari, kuma nan bada jimawa ba za’a fara gina wasu hanyoyi a sauran kasuwannin jihar, musamman a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da za’a fara a 2017.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya kuma yi watsi da babatu da wasu ke yi game da aikin samar da tashar jirgin kasa da jihar ke shirin yi kan kudi Dala bilyan $1.85 cewa aiki ne da zai samar da kudaden shiga ga jihar shi ya sa suka bawa aikin muhimmanci.