Gwamnatin Kano Ta Yaba Wa Dankwangilar Gadar Kasa Ta Panshekara


ganduje

 

Gwamnatin Kano ta yaba da yadda aiki gadar kasa ta Panshekara da ke kwanar Madobi a cikin birnin Kano ke tafiya.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin kwamishinan ayyuka, gidaje da sufari na jihar, Alhaji Shehu Haruna a lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta ma’aikatar ayyuka don duba ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa a jiya Talata

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, aikin gadar wanda kirkiran wannan gwamnati ce ta Ganduje ta kai kusan kaso 90 na kammaluwa.

Alhaji Haruna ya yaba wa dan kwangilar bisa kwazonsa tare kuma da yin kira ga wadanda suka kafa tireda a karkashin gadar da su kwashe kayansu

Kwamishinan ya ce, in aka kammala gadar, za a samu saukin cunkoson ababen hawa a wannan hanyar

 

panshekara

You may also like