Gwamnatin Kano Tasa Hannu Akan Kwangilar Gina Hanyoyin  Jirgin Kasa A Fadin Jihar na Kimanin Kudi ($1.8bn)



Gwamnatin Kano Tasa Hannu Kan Kwangilar gina hanyoyin jirgin kasa a cikin Jihar da wani kamfanin  Gina Titunan Jirgin Kasa Na Kasar China mai suna C18.

Hanyoyin zasu bi ta wadannan Bangarorin garin kano:

Jogana – Bata 

Dawanau – Bata 

Janguza Zuwa Bata Da kuma 

Kwanar Dawaki – Bata

Kwangilar dai wadda zata dauki tsawon shekaru 4 anayi,  an raba zuwa bangarori guda biyu,  bangaren Farko na aikin zai dauki shekaru 2, sannan daya bangaren ma zai dauki shekaru biyu anayi. 

 Gwamna Ganduje ya kara da cewa anyi hakan ne don samar da saukin tafiye tafiye a cikin Jihar da kuma kawo karin kudin shiga ga jihar, sannan ya kara da cewa,  aikin yana daya daga cikin shirye shiryen gwamnatin sa na mayar garin kano daya tamkar da dubu. 

Bankin Na Kasar china shi zai biya kaso 85 cikin dari na kudin aikin sannan ita gwamnatin kano zata biya ragowar kaso 15

Bangare na Farko na aikin Wato Dawanau Zuwa Bata Zaici kimamin kudi dala miliyan 555 ( $555 billion ) . 

Shugaban kamfanin da zasi aikin Mr Ben Shinxo Ya tabbatar da cewa Kamfanin Sa zasu gama wannan aikin a iya shekarun da aka deba musu. 

You may also like