Gwamnatin jihar Katsina za ta ɗauki ƙarin sababbin likitoci 54 aiki, ma’aikatan jiya 600 da kuma sauran ma’aikatan kula da lafiya a asibitocin jihar.
Gwamna Aminu Bello Masari wanda ya bayyana haka a ƙarshen mako ya lura cewa yinkurin daukar ma’aikatan zai inganta harkar kula da lafiya a jihar.
A cewarsa zuba jarin da gwamnatinsa take a fannin lafiya ya na haifar da ɗa mai ido domin tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin ganin likita ya ragu sosai.
Gwamnan ya ƙara da cewa sababbin na’urorin da gwamnatinsa ta saka a Asibitin ƙwararru na Amadi Rimi sun ƙara inganta fannin kula da lafiya a jihar.