Gwamnatin Katsina Za Ta Kaddamar Da Hukumar Kula Da Zirga-Zirgan Ababen Hawa


 

 

Majalissar dokokin jihar Katsina ta gabatar da wata doka karo na biyu domin, kafa hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa a duk fadin jihar da ake kira ( Katsina State Security And Road Traffic Authority ‘KATSROSA’ )

Hukumar za ta sa ido sosai a duk fadin jihar domin ganin ana bin ka’idojin tuki, musamman wajen tsayawa da wucewa idan na’urar bada hannu ta bada umurnin wucewa ko tsayawa.

An dai yi wa dokar karutu na biyu, bayan da mataimakin masu rinjaye na majalissar Hon. Abubakar Korau ya gabatar da kudurin, in da ya ce kafa dokar za ta kara taimakawa matuka wajen ganin ana tafiyar da tuki yadda ya kamata tare da samun kiyaye afkuwar hadura a jihar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like