Gwamnatin Kebbi Ta Sauke Wasu Kantomomin Kananan Hukumomi


abubakar-atiku-bagudu-kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya amince da sauke duk Kantomomin riko na Kananan Hukumomi 17 ‎daga cikin 21 da ke jihar.  Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwasanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da ‘yan jarida na ofishin Gwamnan, Alhaji Abubakar Mu’azu Dakingari. Inda ta bayyana cewa Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi wata ganawa da Kamtomomin masu barin gado a fadar gwamnatin a daren Larabar nan da ta gabata.

Gwamna Bagudu ya ce, su Kamtomomin Kananan Hukumin Kalga, Arewa-Dandi, Koko-Besse da Fakai za su ci gaba da mulkinsu saboda wa’adinsu bai kare ba. Amma Kamtomomi guda 17 da wa’adinsu ya kare, bisa ga dokar da ‘yan Majalisar Dokokin jihar suka sanya wa hannu, ya zama wajibi a saukesu.

Wadanda abin ya shafa sun hada da Kananan Hukumomin, ‎Birnin Kebbi, Jega, Maiyama, Aliero, Bagudo, Gwandu, Suru,Yauri, Shanga, Ngaski, Zuru, Danko-Wasaga, Sakaba, Dandi, Argungu, Augie, da Riba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like