Gwamnatin Kogi Ce Ke Da Alhakin Sace Sandar Majalissa – Jaridar Blueprint


Sabbin rahotanni na ci gaba da bullowa game da badakalar sace sandar majalisar Dattawa inda wata majiyar jaridar ” Blueprint ” ya nuna cewa Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ne ya dauki nauyin sace sandar majalisar.

Majiyar ta nuna cewa daga cikin ‘yan dabar da kama, sun fito ne daga garin Okene da ke cikin jihar Kogi kuma bayan sun sace sandar, sun zarce ne zuwa ofishin Hulda da jama’a na gwamnatin jihar Kogi da ke Abuja.

You may also like