Gwamnatin Kogi ta saka dokar hana fita a ƙananan hukumomi 5 


Gwamnatin jihar Kogi ta ayyana dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a kananan hukumomi biyar dake mazabar majalisar dattawa ta Kogi ta Tsakiya.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Adavi, Ajaokuta,Okene,Okehi da kuma Ogori/Magongo .

Petra Akinki Onygbule jami’ar yada labaran gwamna Yahaya Bello ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar.

Babu wani dalili da aka bayyana na daukar wannan mataki wanda aka dauka da yammacin ranar Laraba.

“Wannan sanarwa ce ta hana fita  tsawon sa’o’i da aka saka a kan kananan hukumomi biyar dake mazabar Kogi ta Tsakiya daga karfe 12 na dare nan da awa daya kenan,” sanarwar tace.

“Wannan dokar hana fita za ta kai tsawon awanni 24, babu zirga-zirga ko wace iri a tsawon wannan lokaci ,”

“Dukkannin waɗanda suke zaune a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta Okehi,Okene Ogori/Magongo ana shawartarsu su bi wannan umarni.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like