Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Daukar Sabbin ‘Yan Sanda 10,000 Duk Shekara Gwamnatin Najeriya ta ba wa rundunar ‘yan sandan kasar, daukar sabbin jami’ai dubu goma a duk shekara, domin kawo karshen rashin yawan jami’an tsaron da kasar ke fuskanta. 

Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris ya tabbatar da samun cigaban, yayinda yake jagorantar wani taro da manyan jami’an ‘yan sanda a birnin Abuja.

You may also like