Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakan Gaggawa Kan Rahoton Bullar Cutar Ebola



Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya bayar da umarnin ga dukkan ma’aikatan lafiya da ke aiki a asibitocin kan su sa ido ga duk wanda ke fama da zazzabi don tantance yanayin zazzabin cutar Ebola.

Ministan ya kuma shawarci al’ummar Nijeriya kan su rika wanke hannayensu a kan kari tare da kai rahoton duk wanda ke fama da zazzabi a asibiti mafi kusa. Wannan umarni da Ministan ya bayar ya zo ne bayan da Kungiyar Kiwon Lafiya ta tabbatar da ta sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar dimokradiyyar Kongo.

You may also like