Gwamnatin jihar Neja ta nuna fushinta ga kamfanin bada wutar lantarki na AEDC kan yadda ake karancin wutar lantarki a duk fadin jiha duk da cewa manyan tashoshin samar da wutar lantarki na aje ba, Kainji da Shiroro duk a cikin jihar suke.
Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Ahmed Ketso ya ce abisa kasancewar wadannan manyan tashoshin wutar lantarkin, ya kamata ne a rika samun wutar lantarki na awowi ashirin da hudu a jihar inda ya nemi kamfanin AEDC ya gaggauta kawo karshen wannan matsalar.
A bangarensa, Shugaban kamfanin AEDC, Injiniya Earnest Mupwaya ya koka ne kan yadda masu Hulda da kamfanin ba su son biyan kudin wuta inda ya ce a halin yanzu kamfanin na bin bashin Naira Bilyan 40. Ya ce kamfanin zai rika samar da wadataccen wutar lantarki da zarar mutane suka fara biyan kudin wuta akai akai.