Gwamnatin Saudiyya ta daina aiki da Kalandar Musulunci


 

 

Gwamnatin kasar Saudiyya wadda ke amfani da Kalandar Musulunci a ranar Lahadin nan ta koma amfani da tsarin Kalandar Miladiyya kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi.

Kalandar Musulunci na da karancin kwanaki 15 idan aka kwatanta ta da Kalandar Miladiyya mai kwanaki 365 a shekara, kuma hakan zai taimakawa Saudiyyan wajen ajje kudade ta hanyar yanke albashin ma’aikatanta da dama.

Kafar yada labarai sun rawaito cewa, Saudiyya ta fara amfani da Kalandar tun shekarar 1932 bayan an kafa kasar.

Amma sakamakon matsalolin kudi da neman hanyoyin magance su ya sanya kasar sakin layin da ta ke kai tare da komawa amfani da kalandar Miladiyya.

A yanzu ma’aikatan Saudiyya za su dinga aiki sosai kafin su sami albashi wanda da ma tuni gwamnati ta yayyanke.

Ma’aikatan kasar za su karbi albashi kasa da yadda suka saba karba a baya.

Wannan matakai ya biyo bayan sanarwar da Majalisar Zartarwar kasar ta bayar na rage albashin ministoci da mambobn Shura masu ba wa gwamnati shawara.

Kasar Saudiyya dai na daukar matakai daban-daban wajen magance matsalar tattalin arziki da ke damunta sakamakon karyewar farashin albarkatun man fetur.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like