Gwamnatin Sokoto Ta Raba Naira Miliyan 31 Ga Mutane 775


 

Gwamnatin jihar Sokoto ta raba kudaden da jimilarsu ya kai Naira miliyan 31 ga iyaye 775 don su dau nauyin ilimin ‘ya’yansu

Kwamishin tsare-tsare da kasafin kudi na jihar ta Sokoto, Bala Kokani ya bayyana wa manema labarai da ya gabatar a Sokoto

Wannan tsari a cewar kwamishina Kokani, na daga cikin tsare-tsaren da jihar ta shirya don cimma burinta na samun nasarar shirin Muradan Karni .

Kokani ya ci gaba da cewa tuni dai kwamitin tsara kasafin kudi na jihar Sokoto ta yi nisa wajen tsare-tsaren kasafin kudin shekarar 2017

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto a karkashin jagorancin Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da kasafin kudinta na shekarar 2016 tare da bayyana cewa kasafin 2017 zai zo da manyan ayyukan raya kasa da na more rayuwa sama da wanda aka cimma a bana

Kokani ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto ta bude shafi a yanar gizo da zai ke nuna nasarorin da jihar ta samu a shirinta na Muradan Karni

You may also like