Gwamnatin Sokoto Ta Yi Zama Don Cimma Yadda Za’a Wadata Jihar Da Man Fetur Gwamnatin jihar Sokoto da Kungiyar masu sayar da man fetur na jahar sun cimma matsaya kan yadda za a samarda man fetur. 
Jihar Sokoto da Kungiyar masu sayar da man fetur mai zaman kanta reshen jihar Sokoto (IPMAN) sun cimma yarjejeniyar cewa dukkaninsu za su tabbatar da cewa an samar da man fetur a kan kayyadadden farashi a ko ina cikin jihar. 
Gwamnatin jihar ta ce za ta karbe takardar mallaka ta duk wani gidan sayar da man da ke boye fetur ko,sayar da shi fiye da farshin da aka kayyade, yanayin da ya sa aka samu matsalar karancin man fetur ta fiye da sati biyu a jahar ba gaira ba sabab
An dai yi yarjejeniyar ne a lokacin wata ganawa tsakanin Gwamnan jahar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, da Kungiyar masu sayar da man fetur ta kasa reshen jahar Sokoto (IPMAN)  wadda Suleiman Magaji yake jagoranci, da mambobin kwamitin samar da man fetur na jaha
Da yake magana a lokacin ganawar , Tambuwal ya ce gwamnatin jahar za ta bayar da wurin ajiye man ta ga yan kasuwar domin su samu isashen wurin ajiye man da za su rarraba ma gidajen mai
“Muna da wurin ajiye mai da ke daukar lita miliyan daya da dari takwas a nan Sokoto, zamu  bari kuyi amfani da wurin ku ajiye man da zaku rarraba wa gidajen man ku, domin tabbatar da jama’a sun same shi a kan farshi mai rahusa ”
“Kwanakin baya an yi min cikakken bayani kan kalubalen da kuke fuskanta musamman wurin biyan bashin da ake bin gwamnatin tarayya.  A matsayin mu na gwamnati za mu gabatar da matsalar ku a Abuja domin mu tabbatar da an biya ku.” Gwamna Tambuwal 
Gwamnan ya jadda cewa duk gidan man da aka kama ya boye man zai fuskanci fushin hukuma. 
 A na shi jawabi, shugaban kwamitin samar da Mai na jahar Sokoto Ibrahim Magaji Gusau ya ce manbobin kwamitin  za su yi duk abin da ya kamata domin tabbatar da an magance matsalar karancin mai, a jahar
“Ina sanar da ku cewa, duk wata tankar mai da aka turo Sokoto za a saukar da shi a kuma sayar dashi ga jama’a ba tare da bata lokaci ba, haka kuma dukkanin manyan yan kasuwar man fetur da ke Abuja da Lagos  yan asalin jahar Sokoto , za a jawo su, su taimaka don a magance wannan matsalar. ” Magaji 
Shugaban  kwamitin haka ma ya yabawa gwamnatin jahar kan shaawar da ta nuna na tabbatar da an shawo kan matsalar man fetur da ake fuskanta.

You may also like