Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi watsi da zargin barnar dukiyar kasa


 

000_was4080728

Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta yi watsi da wani rahoton mai rajin kare hakkin dan’adam George Clooney, da ya fitar a Amurka, wanda ya nuna cewa bangaren gwamnati da na ‘yan tawaye suna tabka cin hanci da rashawa tare da amfani da rashin zaman lafiyar kasar wajen azurta kansu.

Kakakin gwamnatin shugaban kasar Salva Kirr, Antony Wek yace rahoton bashi da wani sahihanci illa batanci ga gwamnatin Sudan ta Kudu da kuma nuna son zuciya.

Wek ya ce mai yiwuwa gwamnati ta dauki matakin shari’a kan wannan rahoto.

Shima dai madugun ‘yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar ya musanta zargin da rahoton ya yiwa bangarensa, inda ya nisanta kansa da satar dukiyar kasar.

You may also like