Gwamnatin tarayya bata da kudin kammala aikin kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta -Bawa


Abubakar Bawa, karamin minista a ma’aikatar, ma’adanai da sarrafa karafa ya ce gwamnatin tarayya bata da kudin da zata kammala aikin kamfanin sarrafa karfe na Ajaokuta dake jihar Kogi.

Ya bayyana haka a ranar Litinin lokacin da yake magana a wurin zaman sauraron jin ra’ayin jama’a da kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta kafa akan kamfanin ya shirya.

Abubakar ya fadawa yan majalisar cewa jingina itace hanyar da tafi da cewa wajen farfado da kamfanin.

“Gwamnati har rancen kudi take domin gudanar da ayyukan yau da kullum hakan na nuna muku cewa babu kudi,”ya ce.

Shugaban kwamitin, kuma shugaban masu rinjaye na majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce Najeriya za ta iya kammala kamfanin kuma jinginar da shi na nufin yin asarar biliyoyin daloli da aka kashe a aikin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like