Gwamnatin Tarayya Da Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta ASUU Sun Cimma Matsaya


Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU ta cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Cimma yarjejeniyar ya biyo bayan taron da wakilan kungiyar sukayi da na gwamnatin tarayya wanda ya dauki tsawon awanni 12 ana gudanar dashi.

Da yake magana da yan jaridu bayan kammala taron, shugaban kungiyar ta ASUU, Biodun Ogunyemi, yace taron ya haifar da da mai ido kuma zasu koma su sanar da sauran rassan kungiyar dake Jami’o’i kafin su janye yajin aikin da suke yi.

 Shima da yakewa yan jaridu bayani ministan ilimi Mallam Adamu Adamu, yace tuni aka amince da wasu daga cikin bukatun kungiyar kuma zasu janye yajin aikin da suke a sati mai zuwa.

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ta tsunduma yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta biyo bayan gazawar gwamnatin na kin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma da kungiyar a shekarar 2009.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like