Gwamnatin Tarayya Ta Aiyana Ranakun Litinin Da Talata A Matsayin Ranakun Hutun Karamar Sallah Gwamnatin tarayya ta aiyana ranakun Litinin 26 da Talata 27 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutun karamar sallah. 

Ministan cikin Abdulrahman Bello Dambazau, ne ya bayyana haka a madadin gwamnatin tarayya cikin wata sanarwa da darakta mai kula da ofishin babban sakataren ma’ikatar, Dakta Rufa’i Kawu Attahiru ya sanyawa hannu a jiya Alhamis. 

Ministan yayi kira ga dukkanin musulmi da ma yan Najeriya baki daya  da suyi amfani da shagulgulan bikin sallah ,wajen yiwa kasa addu’ar zaman lafiya da hadin kai. 

Dambazau ya kuma shawarci yan Najeriya dasu kaucewa kalaman da ka iya kawo rabuwar kai,kana Ai hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari wajen gina dunkulalliyar kasar Najeriya  mai cike da zaman Lafiya.Wacce zata bawa kowa yan cinsa,ciki har da na zama a duk inda yakeso kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. 

  Ministan ya kara tabbatar da jajircewar gwamnatin wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin yan Najeriya,yace gwamnati tana da karfin da zata tura jami’an tsaro  don maganin duk wani mutum dazai kawo barazana ga dorewar kasarnan. 

Ya kuma bawa yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin zata yi adalci ga kowa. 

You may also like