Dillalan mai sun bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya kan biyan bashin biliyan ₦650 na tallafin mai.
Kungiyar dillalai da kuma masu wuraren ajiye mai ta DAPPMAN da kuma ta manyan dillalan mai da ake kira MOMAN sun rubuta wasika ga shugaban kasa Muhammad Buhari da kuma karamin ministan mai Ibe Kachikwu a ranar 24 ga watan Janairu kan bashin da su ke bi.
A wasika ta biyu dillalan sun isar da sakon matakin da suka yanke na fara korar ma’aikata masu yawa da kuma fara rufe wuraren ajiyar mai cikin kasa da ma ka makonni biyu.
Amma a wata sanarwa mai dauke da sa hannun hadin gwiwa na shugaba da kuma sakataren kungiyar DAPPMAN, ta ce an gudanar da doguwar tattaunawa tsakaninsu da kamfanin NNPC, ma’aikatar Kwadago da kuma fadar shugaban kasa.
Dillalan sun bayyana fatansu cewa majalisun tarayya za su amince da batun biyan kudin domin kawo karshen matsalolin da suke fuskanta.