Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar juma’a  a matsayin hutun mauludi


Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a a  matsayin ranar hutun mauludi.

Abdulrahman Dambazau, ministan harkokin ciki gida ya bayyana haka a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da aka fitar yau Laraba a Abuja.

Sanarwar mai dauke da sahannun, Abubakar Magaji, babban sakatare a ma’aikatar cikin gida.

Sanarwar ta ce Dambazau ya shawarci dukkanin musulmi dama yan Najeriya baki daya da suyi amfani da lokacin wajen yin addu’ar samun zaman lafiya, cigaba da haɗin kan kasa.

 Ya kuma shawarci yan Najeriya da su goyi bayan gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari a kokarin da take na gina kasa.

You may also like