Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata,29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu, domin bikin Ranar Dimakwaradiya ta shekarar 2018.
Ministan cikin gida,Abdulrahman Dambazau shine ya bayyana haka jiya a Abuja, a madadin gwamnatin tarayya , ya taya yan Najeriya murna game da bikin tare da bada tabbacin alkawarin gwamnati na cigaba da karfafa dimakwaradiya.
A wata sanarwa mai dauke da sahannun babban sakatare a ma’aikatar, Dakta M.B Umar, ministan ya shawarci dukkanin yan Najeriya da su cigaba da yarda da kuma bawa gwamnati goyon baya a kokarin da take na gina kasa dunkulalliya mai cike da zaman lafiya bisa diga-digan dimakwaradiya.
Ranar 29 ga watan Mayu na kowacce shekara rana ce da aka ware domin bikin tunawa da ranar da kasarnan ta dawo mulkin farar hula tun daga shekarar 1999.