Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar gina hanyar jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kaduna


Gwamnatin tarayya ta amince da kwangilar aikin gina layin dogo na zamani daga Ibadan zuwa Kaduna kan kuɗi dala biliyan $6.7 .

Rotimi Amaech, ministan sufuri, yace aikin wani ɓangarene na aikin gina layin dogo daga Ibadan  zuwa Kano.

Ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa tarayya.

Amaechi ya ce gwamnatin ta kuma amince da gina wani layin dogo da zai haɗa Ado-Ekiti da kuma Osogbo.

“Majalisar zartarwa ta amince da sake bada kwangilar gina layin dogo daga Ibadan zuwa Kaduna.kun san tun farko majalisar zartarwa ta amince da kwangilar gina layin dogo daga Kano zuwa Kaduna saboda haka yanzu gabaki daya daga Ibadan zuwa Kano an bada kwangilar aikin,”ya ce.

“Kwangilar da aka amince da ita yau ita ce daga Ibadan zuwa Kaduna kan kuɗi dala biliyan $6.7. Wannan tsohuwar kwangila ce da aka fara bayar da ita a shekarar 2006.”

You may also like