Gwamnatin tarayya ta bada umarnin gudanar da bincike kan yadda wasu yandaba suka samu damar shiga zauren majalisar dattawa har ta kai ga sun dauke sandar majalisar.
Lai Muhammad, ministan yada labarai shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar a Abuja.
Sanarwar ta ce gwamnati ta kadu matuka da samun labarin sace sandar majalisar dattawa.
Ovie Omo-Agege, sanata mai wakiltar mazabar Delta ta tsakiya, wanda majalisar ta dakatar a makon da ya gabata, ne ake zargin ya jagoranci wata tawagar yan daba ya zuwa cikin harabar majalisar.
Wadanda suka raka Omo-Agege, su ne suka sace sanda daga baya.
Muhammad ya ce za a kara tsaurara matakan tsaro a ginin majalisar domin kare faruwar haka a nan gaba.