Kafin rasuwarsa, Marigayi Abu Ali shi ne Kwamandan da ke jagorancin Sojojin Nijeriya da ke Malam Fatori wanda ke yankun Arewa maso gabashin kasar nan.
Marigayin ya rasu ne a bakin daga lokacin da suke fafatawa da ‘yan Boko Haram a ranar 4 ga watan Nuwamban da ya gabata.