Gwamnatin tarayya ta Bayyana ranar 3 ga watan oktoba a matsayin ranar zagayowar ‘yancin Kai. 


Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun bikin zagayowar ranar da Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga hannun Turawan Mulkin Mallaka.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurahman Danbazau ne ya sanar da haka inda da ya taya al’ummar Nijeriya murnar wannan rana wanda shi ne na karo 56 yana mai bayar da Tabbaci kan cewa gwamnati ta fara bin wasu matakai na rage radadin talauci da ya addabi al’ummar kasar nan.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like